<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>422</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) In na sami dukan kome na duniya
 Wannan da amfani ne, in ba ni da ceto?
 A cikin zuciya in ba salama
 Me za a yi da kayan duniya?
 Ko na sami duniya, amma ba ceto
 Gwamma ba a haife ni da na shiga Jahanama.

[V2]
 KORUS
 Ba ni Yesu, O ba ni Yesu
 Kullum, har abada, O ba ni Shi.

[V3]
 2)Ko na sami dukiya cikakkiya
 Da suna sannanu ga dukan mutane
 Amma babu bege ko wurin sabka
 Ina amfaninsu a sa'annan?
 Ba shakka Allah ba zai yi wargi ba.
 Yanzu ka taimake ni in yi tunani.
 Korus

[V4]
 3)Duk walaha ce in ba tare da Yesu
 Ɓatace ne ni cikin zunubaina
 In har abada ba ganin haske
 Dufu kaɗai da zafin kuka
 Ko na zama nan ba bukatar Yesu
 Ran da na mutu fa, ina dabarata?
 Korus

[V5]
 4) Murna ba misalinta wurinsa
 Maganin baƙin ciki, ɓa'a azaba
 Ba zunubi da ya ƙi yin wanke
 Ko wahala da ba za ya ji.
 In na zama ni kaɗai da Yesu
 Ba kome ba ne, shi ne bukatata.
 Korus</lyrics>
<title>In Na Sami Dukan Kome na Duniya LW422</title>
</song>